Segment
Invitation to Know Jesus Personally
6 minFHD
JESUS·61 of 61Clip 61 of 61
Invitation to Know Jesus Personally
A narrator gives an invitation to know God personally. The invitation is open to everyone. It means turning to God and trusting Jesus with our lives and to forgive our sins. We can speak to Him in prayer when we're ready to become followers of Jesus.
QuestionsRelated Questions
Ask yoursBible Quotes
ShareTranscript
Hausa ( حَوْسَ)
Cikin littafi mai tsarki Allah ya shaida Almasihu zaizo ya ceci dukkan duniya
Rayuwar Yesu ta shaida lallai shi ne annabawa suka yi zancen zuwan sa
Annabi Ishaya yace wata budurwa zata yi ciki ta haifi ɗa
Bayan shekaru da dama haihuwar Yesu ta cika wannan annabcin
Littafi mai tsarki yace mai tsarkin nan da za'a haifa za'ace da shi ɗan Allah
Wato za'a kira Yesu ɗan Allah ba ɗa na jikiba amma ɗa na ruhu
Hakan ya bayyana ta wurin rayuwarsa
Ya warkar da masu cuta
Ya gafarta zunubansu ya shirya su da Allah
Ya kuma alƙawarta musu mulkin Allah na har abada
Ya bada kansa hadaya domin zunuban su ya tashi daga matattu
Yesu yace ba me karɓe mini rai don kaina nake bada shi
Rayuwar Yesu ta cika annabcin annabawa ta kuma ƙarfafa gaskiyar maganar Allah
Annabawa sun shaida cewa
Maganar abar dogara ce kuma tabbatacciya ce ya Ubangiji
Yesu yace sama da ƙasa zasu shuɗe amma maganata bazata shuɗe ba
Yesu ya zo ya bamu rai a yalwace
Ganin yadda mutum ya yiwa Allah rashin biyayya a gonar adinin
Mutum ya zaɓi bin hanyar sa wacce ta rabasa da mahaliccin sa
Littafi mai tsarki yace
Ƴan Adam duka sunyi zunubi
Sakamakon zunubi kuma mutuwa ne
Wato mutuwa ta ruhu kenan
Kamar yadda Allah ya tanada rago a maimakon ɗan Ibrahim
Haka Allah ya aiko Almasihu ya mutu a madadin mu
Rayuwa da mutuwa da tashin sa sun mai da dangantaka tsakanin Allah da masu dogara ga Yesu
Yanzu masu bin Yesu ba gafarta zunuban su kaɗai akayi ba
Amma an cecesu daga hukunci
An tabbatar musu da shiga aljanna
Rai da yanci daga ikon zunubi ne Yesu keba kowa a yau
Ba bin wani addini ba amma ana zancen gaskata Yesu wanda yace
Ganinan tsaye a bakin kofa ina ƙwanƙwasawa
Kowa yaji murya ta ya bude kofar sai in shiga wurin sa
Ana nufin mu juyo ga Allah mu dogara ga Yesu ya shigo zukatan mu
Ya gafarta mana ya maishe mu karɓaɓɓu gareshi ba abin marmari ko tunanin sa a zuciya kaɗai ba
Karɓarsa zamu yi da son ran mu ta wurin alheri saboda ban gaskiya
Duk wanda keso yazamo mai bin Yesu Almasihu zai iya magana da shi cikin addu'a
Mai yuwa kana shirye ka buɗe kofar zuciyar ka zaka iya yin wannan addu'ar a cikin zuciyar ka
Ya Yesu
Ina bukatarka
Nagode da mutuwar da kayi don zunubai na
Na furta zunubai na da roƙon gafara
Na buɗe zuciyata na karɓe ka kazamo mai ceto na da Ubangiji na
Nagode domin gafarar zunubai na domin ka bani rai na har abada
Ka maishe ni irin mutumin da ka keso
Yanzu da na zamo cikin masu binka
Ameen
Yesu yayi magana kan masu binsa da cewa
Tumaki na sun san murya ta na sansu suna bina
In masu bin Yesu suna so su samu rai da ya alkawarta
Dole ne suyi addu'a suna karatu da sauraran maganar Allah kullum
Suyi ta zumunci da juna suna shaida shi ga wasu
Tuna da alƙawarin sa
Cewa an mallaka mini iko dukkan sama da ƙasa
Gashi ni kuma ina tare da ku har matuƙar zamani